El Rufa’i Ya Haramta Jami’an Kiyaye Hadura Kan Titunan Kaduna



Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i ya Haramtawa jami’an hukumar Kiyaye hadurra ta kasa binciken masu ababen hawa a kan manyan titinan jihar bayan koken da ake yi game da ayyukan jami’an hukumar.
Kakakin Gwamnan, Mista Samuel Aruwa ya ce an dauki matakin ne bayan wani taron majalisar tsaro ta jihar inda ya nuna cewa ana zargi jami’an hukumar da karba cin hanci da kuma rashin mutunta masu ababen hawa.

You may also like