El-Rufai Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Korar Malaman Firamare Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ba ta da shirin korar malaman makarantun Firamaren nan su 21, 780 da suka kasa cin jarrabawar cancanta da aka shirya masu kwanaki.

Da yake karin haske kan batun, Mataimakin darakta a Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da fasaha, Idris Aliyu ya ce, gwamnati za ta sake bayar da horo ga wasu daga cikin rukunin malaman yayin da kuma za a tura wasu daga cikinsu zuwa wasu ma’aikatu da ake ganin za su yi amfani.

Tun da farko dai, gwamnatin jihar ta nuna cewa za ta sallami dukkan malaman wadanda ba su ci jarrabawar ba, matakin da ya janyo kungiyar Kwadago da na malamai suka gudanar da zanga zangar nuna adawa ga wannan shirin amma kuma Shugaba Muhammad Buhari ya fito fili ya goyi bayan Gwamnan kan shirin farfado da darajar ilimi.

You may also like