El-Rufai: Atiku ba zai kawowa Buhari cikas ba a zaɓen 2019


Hakkin mallakar hoto:Jaridar Daily Trust

Gwamnan jihar Kaduna ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ko da an bashi tikitin tsayawa takara  na jam’iyar PDP to ba zai zamo wata barazana ba, ga shugaban kasa Muhammad Buhari ba a zaɓen shugaban kasa na shekarar 2019.

El-Rufai ya fadi haka a wata ganawa da ya yi da manema labarai dake fadar shugaban kasa bayan ya gabatar da sallar Juma’a tare da shugaban kasa Buhari a masallacin juma’a dake fadar shugaban kasa.

Gwamnan yana mai da martani ne kan ficewa daga jami’iyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasar yayi.

APC na da masaniyar cewa Atiku zai fice daga jam’iyar cikin watan Disamba, hakan ma ya fiye masa da ya tafi da wuri kafin lokacin da ya tsara.

El-Rufai ya bayyana kwarin gwuiwarsa cewa babu wani gwamna ko da  Jibril Bindow na jihar da Atiku ya fito Adamawa da zai bi shi.

You may also like