Elzakzaky ya gana da yan jaridu


Ibrahim Elzakzaky, shugaban kungiyar Yan Uwa Musulmi ta Najeriya da akafi sani da shi’a yace yana nan da ransa kuma yana samun sauki.

Shugaban ya fadi haka  a karon farko ba da ya fito bayyanar jama’a tun bayan da jami’an tsaro suka kama shi a shekarar 2015.

Elzakzaky wanda ke tsare a hannun jami’an  tsaro na farin kaya DSS yayi magana da yan jaridu ranar Asabar a Abuja.

“Ina samun sauki nagode da addu’o’inku,” a cewar shugaban kungiyar ta shi’a .

Elzakzaky ya fada hannun jami’an tsaro cikin watan Disambar shekarar 2015 bayan wata arangama da magoya bayansa suka yi da sojoji a garin Zariya.

Sama da mutane 300 ne ya’yan kungiyar aka rawaito sun mutu a rangamar da suka yi da jami’an tsaron.

A yan kwanakin nan yayan kungiyar sun yawaita yin zanga-zangar da suke kan neman  a sako shugaban nasu.A wasu lokuta har takan kai su da yin arangama da jami’an yan’sanda.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS na cigaba da tsare Elzakzaky duk da umarnin sakin shi da kotu ta bayar.sai dai hukumar tace tana cigaba da tsare shine domin  tsaron lafiyarsa.

You may also like