Erdogan ya ayyana dokar ta baci a Turkiya


Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ayyana dokar ta baci ta watanni uku sakamakon yunkurin kifar da gwamnatinsa da wasu suka yi kuma ya yi alkawarin murkushe duk wasu rassan juyin mulkin da suka rage a kasar.

Ita dai wannan dokar ta baci za ta zama uzurin ci gaba da tsare mutane sama da dubu 10 da aka tsare da suka hada da jami’an tsaro da ma’aikatan shari’a da kuma malaman makarantu.

Ya zuwa yanzu an rufe makarantu sama da 600 a fadin kasar, an kuma kori dubban ma’aikata daga ma’aikatunsu.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kuma haramtawa malaman makarantu barin kasar ko kuma tafiye-tafiye, inda ya ke cewa matakan da ake dauka na gyara ne ba wai taka hakkokin bil Adama ko kuma dimokiradiya ba.

Tuni dai aka gurfanar da Janar Janar na soji 99 da ake zargin cewar su suka kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar juma’a.

Kasashen duniya na sukar dirar mikiyar da gwamnatin ke yi wa jama’a a kasar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like