
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce yana da burin ganin kungiyar ta samu zuwa gasar Zakarun Turai badi.
Ten Hag na fatan hutun gasar cin kofin duniya da aka yi, zai taimaka ma yan wasansa su dora daga inda suka tsaya, wurin ganin sun kare cikin hudun farko.
Ya ma ce watakila su iya lashe sarka a daya daga cikin gasannin da suke ciki.
United ta kai zagayen kwata fayinal na gasar kofin Carabao bayan doke Burnley 2-0, sannan za ta kara da Nottingham Forest a gasar Premier League a Old Trafford ranar Talata.
United na zaune ne na biyar a teburin na Firimiya maki uku tsakaninta da hudun farko, kuma koci Ten Hag ya ce ya shirya yin duk mai yiwuwa, don samarwa kungiyar gurbi a hudun farko kafin kakar wasannin ta kare.
A sauran wasannin na Premir League da ake sa ran za su ja hankali, Arsenal za ta kara da West Ham a wasan hamayya na London, yayin da Manchester City za ta kece reni da Leeds United a Elland road.