
Asalin hoton, Getty Images
Erik ten Hag ya ja ragamar wasa na 50 a Manchseter United ranar Alhamis a Europa League.
Manchester United da Sevilla sun tashi 2-2 a wasan farko zagayen quarter finals da suka fafata a Old Trafford.
Tsohon kociyan Ajax ya karbi aikin horar da United ranar 1 ga watan Yulin 2022, kawo yanzu ya yi nasara 37 da canjaras bakwai da rashin nasara takwas.
Ten Hag ya fara da rashin nasara a wasa biyu a jere a Premier League, inda ranar 7 ga watan Agustan 2022, Brighton ta je ta ci United 2-1 a Old Trafford.
Ranar 13 ga watan Agusta a wasan mako na biyu a Premier League United ta je ta yi rashin nasara a gidan Brentford da 4-0.
Daga nan Ten Hag ya sa kokari ya ci wasa hudu a Premier League a jere da doke Liverpool da Southampton da Leicester City da kuma Arsenal.
Sai kuma ya yi rashin nasara a Europa League a karawar cikin rukuni a Europa League a hannun Real Sociedad.
Kawo yanzu kociyan na kan turbar maye da fiatciyar kungiyar gurbinta a cikin ‘yan gaba-gaba a taka leda a duniya tun bayan Sir Alrx Ferguson.
Ten Hag ya kawo karshen kaka shida da United ta kasa daukar kofi koda na shayi ne, wanda ya lashe Carabao Cup a kakar nan.
Cikin wasa 50 da Ten Hag ya ja ragamar United, kungiyar ta ci kwallo 91 an kuma zura mata 50 a hamsi.
United tana ta hudu a teburin Premier League, gurbin shiga Champions League a badi kenan.
United za ta kara da Brighton a wasan daf da karshe a FA Cup a Wembley ranar 23 ga watan Afirilu.
Haka kuma kungiyar Old Trafford za ta ziyarci Sevilla domin buga wasa na biyu a quarter finals a Europa League ranar 20 ga watan Afirilu.