EU na neman China ta shiga tsakanin yakin Rasha da Ukraine | Labarai | DWBabban jami’in EU a kan harkokin kasashen ketare Enrique Mora wanda ya gana da takwaransa na China Li Hui a birnin Brussels na kasar Belgium ya bukace shi da isar da sakon kungiyar ga mahukuntan Beijing.

China wacce ke zama babbar kawar Rasha ana ganin tana da rawar takawa wajen kawo karshen rikicin da aka shafe watanni 15 ana yin shi.

Kungiyar tarayyar Turai ta ce kasancewar China mamba a kwamitin sulhu na MDD ya kamata ta bada ta ta gudumawar, duk da a cewar a baya China ta nuna ita yar baruwanmu ce a wannan rikicin.

‘Yan siyasar EU na nuna shakku a kan shawarwarin da China ta bayar da ka iya kaiwa ga karshen wannan yaki na Turai.
 

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like