Shugabannin na kungiyar EU sun yi kakausar suka tare da aike wa Moscow da sakon gargadi da ke nuni da girman sakamakon da ka iya biyo bayan wannan matakin nasu.
A cewar mai magana da yawun EU kan manufofin harkokin waje Peter Stano suna ci gaba da duba irin ta’asar da Rasha ke yi a Ukraine, na baya-bayan nan shi ne batun manyan ramuka da aka gano gawawakin daruruwan fararen hula gami da na wasu sojoji da suka yi batan dabo.
Ya zuwa yanzu babu tabbacin karin wasu takunkumai a kan Rasha bisa wannan sabon matakin nata, amma dai Stano ya ce suna ci gaba da yin nazari kan matakan da ya dace su dauka.