Majalisar dokokin kasashen Turai ta goyi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar magance dimamar yanayi da aka cimma a birnin Paris na Faransa, bayan ta kada kuri’ar da ta samu halartar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon a wannan Talata.
Matakin da majalisar dokokin ta dauka zai taimaka wajen gaggauta aiki da yarjejeniyar a duk fadin duniya.
Mambobin majalisar 610 ne suka goyi bayan rattaba hannun, in da 38 suka ki amincewa da haka, yayin da 31 suka kaurace wa kada kui’ar.
Sakamakon kuri’ar dai na nufin cewa, nan da ranar jumma’a mai zuwa, kasashen na Turai za su gabatar da rattaba hannun a gaban Majalisar Dinkin Duniya, abin da zai tinzira sauran kasashen duniya wajen aiwatar da yarjejeniyar ta rage fitar da yaki mai guba.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya yi jawabi a gaban mambobin majalisar fiye da 700 a birnin Strasbourg, in da ya ce musu, suna da damar kafa tarihi ta hanyar jan ragama don samar wa duniya kyakkyawar makoma.
Tuni dai Amurka da China da India da ke kan gaba wajen fitar gurbataccen hayaki suka rattaba hannu kan yarjejeniyar wadda aka cimma a watan Disamban bara, yayin da ake bukatar rattaba hannun daga kasashe 55 da ke fitar da kashi 55 na hayakin a duniya.