EU ta yi tir da harba makami mai linzami a Japan | Labarai | DW



A cewar kakakin kungiyar wannan ba komai bane face takalar fada, wanda ya yi hannun riga da ka’idojin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

EU ta ce dole ne Koriya ta Arewa ta guji harba makamai a sararin samaniyar wasu kasashe, bugu da kari ta kuma bada damar hawa teburin sulhu domin tattauna duk wasu matsaloli da take da su a game da kasar ta Japan.

Kazalika kungiyar ta tarayyar Turai ta kuma bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya duba da ma daukar mataki a kan irin barazanar da wannan harba makamai ke da ga kasashe makwabta da ma batun tsaron yankin baki daya.

Wannan shi ne karon farko a cikin shekaru biyar da Koriyar ke harba wa Japan makami mai linzami, lamarin da ya sa ake tunanin akwai wata jikakiya a kasa.

 



You may also like