EU ta ce za ta yi nazari na tasirin da za a samu sakamakon sayen kamfanin nan na Amirka da ke samar da iri wato Monsanto wanda kamfanin Bayer na nan Jamus ya yi.
EU din ta ce hakan ya zame mata wajibi domin ganin cewar manoma da masu sayen iri da magunguna kashe kwari sun samu zabi na irin abinda suke bukata ba wai ya kasance abu guda kawai za su samu ba sakamakon sayen Monsanto din da Bayer ya yi. A jiya Laraba ce dai aka bayyana cewar kamfanin na Bayer zai saye Monsanto wadda hakan zai kai ga samar da kamfanin da ke harkar kayan noma mafi girma a duniya.