
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tsakiyar Faransa N’Golo Kante mai shekara 31 na shirin tafiya Barcelona idan kwanitraginsa ya ƙare da Chelsea a kaka mai zuwa. (Sport – in Spanish)
Paris St-Germain zai soma tattaunawa da ɗan wasan gaban Argentina Lionel Messi mai shekara 35 bayan irin nasarar da ya samu a gasar cin kofin duniya ganin cewa kwantiraginsa zai ƙare a kaka mai zuwa. (RMC via Mail)
Bayern Munich na da ra’ayin sayen golan Argentina da Aston Villa Emilano Martinez mai shekara 30. (MediaFoot – in French)
Sai dai golan Borussia Monchengladbach da Switzerland Yann Sommer mai shekara 34 yana tattaunawa da Bayern Munich kan yiwuwar komawarsa can bayan da golan Jamus Manuel Neuer ya karya ƙafarsa. (Goal)
Kocin Real Madrid Carlo Ancelottu ya nesantar da kansa daga Brazil inda ya ce yana so ya ci gaba da zama da zakarun Turai. (Rai Radio 1 via Mail)
Akwai yiwuwar ɗan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe mai shekara 24 a ranar Talata ya sanar da cewa zai bar PSG a ƙarshen kaka ganin cewa Real Madrid na nemansa. (Sport – in Spanish)
Barcelona na son sayen ɗan wasan Celtic da Croatia Josip Juranovic mai shekara 27 sai dai kulob ɗin na fuskantar ƙalubale daga Atletico Madrid da wasu kulob-kulob na gasar Firemiya.Sports)
Tottenham na tunanin ɗaukar golan Everton da Ingila Jordan Pickford mai shekara 28 domin maye gurbin Hugo Lloris na Faransa. (Football Insider)
Arsenal za ta soma tattaunawa da ɗan wasan gaban Ingila Bukayo Saka mai shekara 21 kan wata sabuwar yarjejeniya a makonni ko kuma watanni masu zuwa. (Caught Offside)
Akwai yiwuwar tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya maye gurbin kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Faransa Didier Deschamps bayan kashin da suka sha a hannun Argentina. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Arsenal da Leeds duk sun shiga fafutikar neman ɗan wasan gaban Brazil Matheus Cunha mai shekara 23 inda Atletico Madrid ke shirin sayar da shi. (Goal)
Chelsea na da yaƙinin cewa za ta ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan RB Leipzig da Croatia Josko Gvardiol mai shekara 20 duk da suna sane da sauran abokan hamayyarsu na neman shi. (90 min)