
Al’ummar garin Mutunji a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya suna cikin halin zulumi da tashin hankali, bayan asarar rayuka mafi muni da garin bai taɓa ganin irin sa ba.
Rahotanni daga garin sun ce a ƙalla mutum 64 ƴan garin ne suka rasa rayukansu bayan da wani jirgin soja ya jefa bam a wani waje da ƴan bindiga suka yi mafaka.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro ya tabbatar wa BBC cewa dukkan waɗanda suka mutun maza ne, mafi yawan su ƙananan yara, sai kuma matasa da tsofaffi.
“An yi asarar rayukan da ba a taɓa samun yawan hakan ba a rana guda a garin namu kuma baya ga wadanda suka rasa rayukansu da dama sun jikkata,” ya ce.
Ganau din wanda shi ma ya rasa ƴan uwansa da dama, ya ce an kai waɗanda suka jikkatan asibitin garin Dan Sadau da na Gusau ana duba su.
“Mutum 17 suna asibitin Dan Sadau su kuma 12 da suka fi jin munanan raunuka suna asibitin Gusau duk ana kula da su.
Faɗa a kan bazawara
Jama’ar garin na Mutunji sun ce kwana shida da suka wuce ne wasu dabobin ƴan bindiga biyu a garin Randa suka yi rigima a kan wata bazawara “da kowa ke so”.
A kan hakan ne aka samu hatsaniya tsakanin su a cikin daji har aka kashe mutum biyu.
Ganau ɗin nan ya ce wa BBC “to daga nan ne sai wani babban ɗan bindiga ana ce masa Damina, ya ce ai mutanen garin ne suka kashe masa yara a don haka sai ya kwashe ƴan garin har mutum 174, a ciki ya kashe mutum 20.
“A yanzu haka kuma wasu fiye da 150 suna hannunsa. Kuma majiyoyi masu ƙarfi sun shaida mana cewa kisan gilla ya yi wa mutane 20 ɗin.
“Bayan nan ne sai Damina ya ce wa mutanen garin Randa ya yi binciken da ya kamata ya yi kuma ya gano mutanen garin Malele ne suka kashe masa yaran,” ya ce.
Jama’ar garin sun kuma ce hakan ya sa aka kai wa mutanen Malele hari, a yayin hakan ne kuma suka yi wa sojoji kwanton ɓauna har suka kashe tara daga cikin su, suka kuma jikkata huɗu da a yanzu haka suke asibitin Dan Sadau.
Wannan abu da ƴan bindigan suka yi ne ya sa sojojin suka nemi ɗauki daga sojojin sama, su kuma ɓarayin lokacin suna neman mafaka sai suka fada garin garin Mutunji.
Kazalika sun ce hakan ne ya sa sojin saman suka jefa bam a yankin ta jirgin yaƙin da ya gansu, “wanda tashin bam ɗin ne ya hallaka ƴan bindigan da kuma mutanen gari har 64”, kamar yadda ƴan garin suka ce.
Sai dai duk da cewa rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa ta yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama, amma ba ta ce harin ya kashe fararen hula ba.
Harin jirgin yaƙin dai ya sa an yi asarar duk wani abu da ke wajen da bam ɗin ya tashi, kama daga gidaje zuwa shaguna baya ga mutanen da suka mutu kamar yadda rahotanni suka ce.
A yanzu haka mutanen garin da aka sace jama’arsu 174 ɗin sun ce tuni suka fara neman hanoyoyin yin sulhu don a dawo musu da su ba tare da an sake kashe ko guda ba.
Me sojoji suka ce?
Rahotannin wasu kafafen yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito nasarar da rundunar sojin ƙasar ta yi tun daga ranar Asabar a jihar Zamfara.
Sojojin sun ce sun samu nasarar kashe ƴan bindiga da yawa bayan da rikici ya yi ƙamari a garuruwan Malele da Maigoge da Yan Sawayu da Ruwan Tofa da Mai Awaki da Zama Lafiya da duka suke ƙarƙashin gundumar Mutunji a ƙaramar hukumar mulki ta Ɗan Sadau.
Jaridar intanet ta PRNigeria ta ce wata majiyar sirri daga ma’aikatar tsaro ta bayyana mata yadda dakaru suka ƙaddamar da jerin hare-haren sama kan dabobin ƴan bindiga daban-daban a yankin.
Asalin hoton, Getty Images
An dade ana fama da rikice-rikice a jihar Zamfara amma hukumomi na cewa suna kokarin shawo kan lamarin
“Wasu ƴan bindiga da suka shiga garin Mutunji don neman mafaka daga harin sama na sojoji sun gamu da gamonsu. Bayan da aka tabbatar rayuwar mutanen ƙauyen ba ta cikin hatsari sai aka far wa ƴan bindigar da ruwan wuta daga sama.
“Hakan ya sa an yi nasarar hallaka ƴan bindiga fiye da 40 da suka ɓuya a ƙauyen. Wasu fararen hula kaɗan sun ji raunuka amma ba munanan raunuka ba ne,” a cewar majiyar sojin, kamar yadda PRNigeria ta ambata.
Wasu mazauna yankunan dai sun bayyana jin daɗinsu kan nasarar da sojojin suka samu.
Wani matashi ya shaida wa PRNigeria cewa ya kamata sojoji su ci gaba da ƙoƙari don hana ƴan bindigar sakat da kawo zaman lafiya a yankin.
Kazalika rundunar sojojin ta yi watsi da batun wasu mazauna garin cewa ƴan bindigar sun kashe sojoji tara, tana mai cewa soja ɗaya ne kawai ya ji rauni kuma shi ma yana samun sauƙi.