Mako guda bayan fada a Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu har yanzu ana ci gaba da zintar gawakin da ke yashe a kusa da tankunan sojoji da aka kana.
Hakan na faruwa ne mako guda bayan kazamin fafatawa da aka yi tsakanin sojojin da ke gaba da juna bisa neman iko, a kasar da ta balle daga gwamnatin Khartum. Daruruwan mutane ne dai suka mutu a gumurzun da aka yi. A watan Disamban shekara ta 2013 ne, yaki ya barke tsakanin magoya bayan shugaba Salva Kiir da na mataimakinsa Rieck Machar. A watan Aprilun bana ne Rieck Machar ya dawo Juba domin rike mukamin mataimakin shugaban kasa, a wata yarjejeniyar jeka na yika da aka cimma, don kafa gwamnatin hadaka. A wannan Litinin ne aka cimma wata kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta, to amma babu wanda ya san abinda ka iya faruwa a wannan kasar, da ta kasa samun zaman lafiya tun samun yancin kanta.