Fadar Gwamnatin Tarayya ta Musanta Batun Gayyatar Majalisa


 

A makon da ya gabata ne, rahotanni suka cika kafofin yada labara na cewa majalisar dokokin Nijeriya ta gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya bayyanan a gabanta ya amsa tambayoyi akan tabarbarewar tattalin arziki da matakan da gwamnatinsa ke dauka don ganin an samu mafita.

Sai dai Fadar shugaban kasar ta ce sam bata san wannan magana ba. Mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya shaidawa kafar yada labarai ta BBC cewa su ma a kafafen yada labarai suka ji batun.

Ya kara da cewa ba su samu wata takardar gayyata ba daga majalisun dokokin kasar da ta bukaci shugaba Buhari da ya bayyana a gaban ta.

A wani zama na majalisar a makon da ya gabata, ra’ayin ‘yan majalisar daga kowacce jam’iyya ya zo daya akan batun gayyatar shugaban kasar.

Matakin dai na daya daga cikin matakan da majalisar ta dauka domin samarwa kasar mafita akan matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki wanda ya tsananta.

You may also like