Fadar shugaban ƙasa ta gayyaci Kwankwaso da Ganduje


Rabi’u Kwankwaso sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa da kuma gwamna Abdullahi Ganduje, gayyace su zuwa fadar shugaban ƙasa dake Abuja kan rikicin dake tsakanin mutanen biyu.

Ganduje ya kasance mataimakin kwankwaso a tsawon shekaru 8 da ya shafe yana mulkin jihar.

Amma kuma mutanen biyu sun raba gari bayan da Kwankwaso ya miƙawa Ganduje ragamar mulkin jihar.

A ƙoƙarin da mutanen biyu suke na nuna farin jininsu dukkaninsu sun shirya gudanar da taron gangami ranar Talata kuma a wuri guda abinda ya jefa fargabar ɓarkewar rikici a zukatan mutanen dake jihar.

A ranar Litinin gwamnan  tare da rakiyar wasu sanatoci biyu da kuma ƴan majalisar wakilai biyu ya gana da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.

Ganduje yaƙi yarda ya ce komai ga manema labarai bayan ganawar.

Ana sa ran shima Kwankwaso zai gana da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo.

You may also like