Daga fadar shugaban kasa, an gargadi ‘yan Nijeriya game da yiwuwar tsananin karancin abinci da ka iya addabar kasar daga shekara mai zuwa a sakamakon fitar da abincin kasar da ake yi zuwa kasashen duniya.
Yayin da yake hira a gidan rediyon Pyramid a jiya, mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana cewa bukatar kayan abinci a duniya ta karu, al’amarin da ya sa ‘yan kasuwa a Nijeriya ke ta fitar da kayan abincin kasar babu ji babu gani, kuma idan har ba’a tsagaita al’amarin ba, toh akwai yiwuwar kasar za ta fuskanci karanci abinci daga farkon shekara mai zuwa.
Malam Shehu ya bayyanan cewa an shawarci shugaban kasa ne daga ma’aikatar noma da ya janyo hankalin ‘yan Nijeriya game da wannan al’amari
Ya kara da cewa akalla tirela 500 na kayan abinci daga Nijeriya ke barin kasar kowanne sati, ya kuma dora alhakin al’amarin akan ‘yan kasuwannin Dawanau a Kano, Maigatari a Jigawa, Bama a Borno, Ilela a Sokoto, da kuma wasu kasuwanni guda 3 a jahar Kebbi.
Ya ce wannan al’amari zai ci karo da manufar Shugaban kasa Buhari na ganin cewa Nijeriya ta dogara da kanta a bangaren samar da abinci, a don haka ya roki ‘yan Nijeriya da su sanya hannu wajen tabbatar da hakan ba ta faru ba.