Gwamnatin tarayyar ta yabawa Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa namijin kokarin da yake yi na yin ayyuka tukuru domin bunkasa jiharsa.
Yabon dai ya fito ne daga fadar shugaban kasan a yau Juma’a jim kadan da fitowar Gwamnan daga wata ganawar sirri da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Aso Villa.
A cewar mai taimakawa shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai Alhaji Bashir Ahmed Gwamnatin tarayya tana sha’awar irin aikace-aikacen da Gwamna Ganduje keyi musamman gadar kasa da sama da yake ginawa a hanyar Madobi dake jihar Kano wacce babu irinta a Nijeriya.