Fadar Shugaban Kasa Tayi Raddi Ga Sule Lamido Fadar Shugaban Kasa ta bayyana tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido a matsayin gigitaccen mutum bayan ya nuna adawa ga shirin yaki da rashawa na gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari.

Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya nuna cewa a zamanin mulkinsa, tsohon gwamnan ya yi amfani da asusun ajiyar Bankin ‘ya’yansa wajen karkatar da kudaden gwamnati amma kuma don rashin kunya an wayi gari shi ne ke sukar shirin yaki da rashawa kuma har ya fito ya nuna sha’awar tsayawa takarar Shugaban kasa wanda a cewar Kakakin irin hakan ya sa kasashen waje ke wa Nijeriya  dariya.

Ya kara da cewa, hukumar EFCC ce ke jagorantar yaki da rashawa kuma a lokacin mulkin PDP ne aka Kirkiro da hukumar amma kuma Shugaba Buhari bai rusa hukumar ba a maimakon haka a kullum kokari yake yi ya karfafa ta don samun nasarar yaki da rashawa. Tsohon Gwamnan dai ya caccaki Buhari ne kan shirin yaki da rashawar da gwamnatinsa ta kaddamar inda ya bayyana shirin mara amfani.

You may also like