Fadar Shugaban Nigeria Ta Musanta Cewa Buhari Ya Ba Wa Clinton Dala Miliyan 500


 

Fadar shugaban Nigeria ta musanta cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ba wa tsohuwar ‘yar takarar shugabancin Amurka da ta sha kaye Hillary Clinton taimakon Dala Miliyan 500 a lokacin da take yakin neman zabe.

Kakakin shugaban Nijeriyan Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga wannan labarin inda ya ce babban abin bakin ciki ne yadda aka kirkiri wannan karyar da jingina ta ga shugaba Buharin.

Malam Garba Shehu ya ci gaba da cewa: Shugaba Muhammdu Buhari ba shi da irin wadannan makudan kudi da zai ba da su. Kuma ko da masa akwai su, shugaba Buharin ba mutum ne da zai ba da su a matsayin gudummawar (zabe ba), saboda me zai bayar”.

Kakakin shugaban na Nijeriya ya kara da cewa ai gwamnatin Nijeriya ne ma take jiran karbo wasu kudaden daga Amurka wadanda aka sace daga Nijeriyan aka cibge a can.

A kwanakin baya ne dai wata kungiya mai suna “The American Black Group for Democracy” ta yi zargin cewa shugaba Buharin ya ba wa Mrs. Clinton gudummawar dala miliyan 500 don yakin neman zabenta.

You may also like