Hukumar aikin haji ta kasa ta ce tana daukar matakan ganin maniyyata aikin hajjin bana sun samu damar biyan kudin aikin.
Da alama dai biyan kudin kujerar zuwa aikin hajjin bana zai yi wa mafi yawancin maniyyatan na bana wuya, saboda yadda darajar naira ta ke a yanzu.
Wannan ne ya sa hukumar ta ce ta fara daukar wasu matakai domin ganin ta rage wa maniyyatan tsadar da take ganin kujerar hajjin za ta yi.
Kamar yadda hukumar ta shaida ta bakin jami’in yada labaranta Alhaji Uba Mana.