Fafaroma Francis ya buƙaci ƙasashe su kyale Afirka



.

Asalin hoton, EPA

Jim ƙadan bayan saukar sa a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Fafaroma Francis ya gabatar da jawabi mai cike da Alla-wadai na yanda ake cin dunduniyar ƙasar da ma nahiyar Afirka na tsawon ƙarni.

Ya kuma yi magana kan mamayar siyasa da ke janyo ɗebe tattalin arzikin ƙasashen da mayar da mutane bayi.

A wani bangare na jawabinsa, ya faɗa wa ƙasashen duniya da su san da irin bala’o’i da aka haddasa a ƙasar da kuma girmama mutanen wurin.

“A kyale Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, a ku kuma kyale Afirka da daina gallaza mata, ba ma’adinai ba ne da za a ce za a ɗebe ko kuma wuri da za a yi wa ganima,’’ in ji Fafaroma Francis, yana mai nuni da ɗimbin albarkatun ƙasa da suka jawo rikici da kuma mutuwa a ƙasar.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like