Fafaroma ya bukaci matasa su yi juriya


Babban jagoran Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya bukaci matasa ‘yan darikar, da su kasance masu juriya domin su shawo kan matsalolin da duniya ke fuskanta.

image

Fafaroma Francis yayin taron matasa a Polan

Fafaroma Francis ya yi wannan kiran ne a yayin bikin rufe taron bikin matasa na duniya da aka kammala a kasar Poland. Tun da fari Fafaroman ya bukaci matasan Kiristocin mabiya darikar Katolika da su kasance masu zama kan teburin tattaunawa da yaki da kalaman nuna kyama da kuma son zuciya. An dai gudanar da bukuwan matasan na duniya ne a dandalin “Field of Compassion” da ke Krakow a kasar ta Poland. A cewar Fafaroma Francis za a gudanar da taron matasan na duniya mai zuwa a Panama a shekara ta 2019.

You may also like