Falalar Salatin Manzon Allah (SAW) A Dare Da Yinin Ranar Juma’a


Yana daga cikin falalar Daren juma’a da yinin juma’a, Manzon Allah (SAW) ya umarnin mu yawaita yi masa salati a wannan lokuta, saboda Hadisin Anas bn Malik (RA) yana cewa: Manzon Allah ( SAW )ya ce:

*(Ku yawaita yi mini Salati a ranar juma’a da daren Juma’a, duk wanda ya yi min salati guda daya, Allah zai yi masa salati guda goma)*

Wasu Daga Cikin Falalar Yiwa Manzon Allah (SAW) Salati:

▪Wanda ya yi Manzon Allah (SAW) salati guda daya Allah zai yi masa salati guda goma*

▪Mafi kusanci da cancanta ga Manzon Allah (SAW) a ranar alqiyama, su ne masu yawaita yi masa salati*
▪Manzon Allah (SAW) yana cewa, ” ku yawaita yi min salati, domin Allah Ya wakilta wani Mala’ika na musamman a wajan Qabarina, babu wanda zai yi min salati face wannan mala’ikan ya ce dani, wane dan wane ya yi maka salati yanzu
▪Manzon Allah (SAW) wani mai zuwa ya zo min daga wajan Ubangijina,sai ya ce; ” Duk wanda ya yi maka salati daga guda daya daga cikin al’ummarka, Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki guda goma, Kuma a kankare masa laifuka guda goma, kuma a daukaka Darajarsa sau goma, kuma a maida masa salatin shima a yi masa

▪Babu wanda zaiyiwa Manzon Allah ﷺ Sallama,face Allah ya mayarmin da ruhina har sai na mayar masa da sallama*

You may also like