Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya. Sanata Shehu Sani zai fuskanci fushin takwarorinsa na ‘yan Majalisa bayan ya fallasa cewa suna karbar alawus alawus na Naira milyan 13.5 a karshen kowane wata.
Rahotanni daga majalisar sun nuna cewa wannan ikirarin na Shehu Sani bai yi wa ‘yan majalisar dadi ba inda suka jaddada cewa Lallai za su dauki mummunar mataki kan Sanata Shehu Sani, domin ya hada su fada ne da mazabun su kan fadi wa duniya abin da ake biyan my duk wata.