Fannin Noma Ya Samar Da Aiyukan Yi Miliyan 6 Ƙarƙashin Buhari


Audu Ogbeh, ministan noma da raya karakara a ranar Litinin yace fannin noma ya samar da aikin yi miliyan 6 cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ministan yana mai da martani ne kan rahoton dake cewa an rasa aiyuka miliyan huɗu tun bayan  da Buhari ya dare kujerar kujerar mulkin ƙasarnan.

Ya bayyana cewa aiyuka miliyan shida da aka samar kuma an samar da su ne a gona da kuma ɓangaren sayarwa da sarrafa amfanin gonar saboda ƙarin yawan noman shinkafa da aka samu.

Ogbeh yayi fadi hakane a lokacin da yake tsefe nasarar da maaikatarsa ta samu da kuma burin da take da shi a shekarar 2018 yayin wani taron sanin makamar aiki da aka gudanar a Abuja.
“Bangaren noma kacokan ya dogara ne da aiki da hannu,amma muka iya samun nasarar rage shigo da shinkafa da kaso 95 cikin ɗari aƙalla hakan ya samar da karin aiyukan yi miliyan 6 a gonaki,” yace.

“Akwai aƙalla yan kungiyar manoman shinkafa su miliyan 12.2, mun  samar da aiyukan yi sama da wanda muka rasa.”

Ministan yace kasarnan ta samu dala miliyan $31 daga cinikin zoɓo a shekarar da ta wuce kuma bukatarsa na dada karuwa.

You may also like