An fara Atisayen Hadin Guiwa Tsakanin Sojojin Kasashen Masar Da Rasha.


4bk873bd78aaddbra4_800c450

A yau lahadi ne sojojin kasashen Rasha da Masar Sun Fara Atisayen Soja

Kamfanin Dillancin Labarun Irna  ya ambato kakakin soja Masar  “Muhammad Samir’ yana cewa; A yau lahadi ne sojojin kasarsa da na Rasha su ka fara gudanar da atisayen hadin guiwa a cikin saharar arewa maso yammacin birnin alqahira.

Samir ya ci gaba da cewa;  Da akwai fiye da sojoji 700 da kuma nau’oin makamai 20 da ake amfani da su wadanda su ke matsakaita. Sai kuma wasu jiragen yaki guda 30 na kasashen biyu.

A gefe daya wata jaridar kasar Rasha, ya buga cewa kasashen biyu suna tattaunawa da juna domin baiwa Moscow damar kafa sansanin soja a kasar Masar.

Sai dai shugaban kasar ta Masar Abdulfattah al-sisy ya karyata cewa da akwai sansanin sojan kasar waje a Masar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like