An fara biyan kudaden alawus ga ‘yan bindiga na Naija Delta


Hukumomi a Najeriya tsun sanar da ci gaba da biyan alawus ga ‘yan bindiga na Yankin Naija Delta da ke cikin shirin afuwar Gwamnati.

0,,16726133_303,00

Wasu dalilai ne dai na neman sulhu suka sa gwamnatin ta Najeriya ta dawo da shirin biyan wannan alawus ga y’an bIndIgar na Naija Delta da a baya suka amince da ajiye makamansu, dalilan sun hada da kokarin gwamnatin na dakile barazanar da ‘yan bindigar ke da ita na aikata munanan laifuka.

Laifukan dai sun hada da fashe-fashen bututayen mai don satar mai din,inda kuma wasu da damansu ke daukar matakin aikata fashi kan teku,da satar mutane don amsar kudaden fansa da dai sauransu a matasyin mataki na uzurawa gwamnartin.Wasu tsofin ‘yan bindigar ma ana ganin rashin biyansu wannan alawus da tsohuwar gwamnati ta marigayi Umaru Musa ‘Yar Aduwa ta saba musu da shi kimanin shekaru biyar baya ,ka iya sa su sake shiga cikin wasu kungiyoyi na tsageru.A yanzu da wannan mataki da gwamnatin ta dauka na ci gaba da biyansu kudaden alawus din zai sa a samu saukin lamarin.

You may also like