An Fara Jigilar Shanu ta Jirgin Kasa Daga Arewa Zuwa Kudancin Kasar nan


 

 

 

A garin Gusau da ke Jahar Zamfara, an kaddamar da sabon shirin jigilar shanu ta jirgin kasa daga yankin arewaci zuwa kudancin kasar.

Bayan kaddamarwar, kimanin shanu 500 ne aka zaunar a cikin jirgin, suka kuma dau hanya zuwa birnin kasuwanci na Legas bayan kaddamarwar.

Wannan wani bangaren ne na shirin da babban bankin kasar ya bullo da shi mai suna NIRSAL, wanda ke da manufar kara adadin kudaden da ake jujjuyawa wajen harkokin noma a kasar da kuma rage yawan asarar da manoman ke tafkawa.

An dai kiyasce cewa cinikayyar shanu tsakanin arewaci da kudancin Nijeriya ya kai na kimanin Naira biliyan 850 zuwa 950 a kowacce shekara.

 

 

cc:alummata

You may also like