Wani kamfani mai suna Innoson Group mallakar dakta Innocent Ifediaso Chukwuma OFR ta fara kera motocin SUV na amfanin rundunar sojojin Nijeriya.
A jiya Laraba, shugaban kamfanin ya gabatar da sabbin motocin kirar IVM G12 ga shugaban rundunar sojojin Nijeriya laftanar janar Tukur Buratai a hedikwatarsu rundunar da ke Maiduguri, a jahar Borno.
An kera motocin ne musamman saboda fatirol da kuma sauran ayyukan sojoji.