Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa yanzu haka ana cikin zaben mutane guda 500,000 wadanda za’a baiwa ayyuka kamar yadda gwamnatin Buhari ta yi alkawari.
Ya fadi haka ne a jiya Talata a Abuja yayin da tawagar Kungiyoyin mata suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.
Ya kara da cewa yayin da ake ci gaba da yin rajista a shirin samar da ayyukan, gwamnati ta fara tantance su domin daukan aiki. Ya ce kusan mutane miliyan daya da dubu dari biyu ne suka yi rajista inda aka rarrabasu zuwa bangarori kamar su malamai, masu taimakon manoma, jami’an fasaha da sauransu.
Ku Karanta Wannan: Jahohin Nijeriya Sun Kasa Biyan Ma’aikata
Haka kuma ministan ya bayyana cewa biyan tallafin dubu biyar biyar ga wadanda basu da aiki zai fara kafin watannan ya kare kamar yadda ministanr Kudi Kemi Adeosun ta bayyana.
Ministan ya jaddad kudirin gwamnati na inganta rayuwa da jin dadin jama’a.