Faransa: An jima ana shiri kafin harin Nice


0,,19410536_303,00

Tuni dai mahukunta a kasar suka tsare mutane biyar da ake zargi sun tallafa wa Bouhlel da ya kaddamar da harin na ta’addanci ta hanyar amfani da bababar mota a birnin na Nice.

Mai gabatar da kara a Faransa Francois Molins ya bayyana a ranar Alhamisd din nan cewa wanda ya kai harin nan a birnin Nice a bikin ranar ‘yanci Mohamed Lahouaiej Bouhlel ya samu taimako kafin ya kaddamar da harin da ya aikata ta hanyar amfani da babbar mota ya tattake jama’a.

Tuni dai mahukunta a kasar suka tsare mutane biyar da ake zargi sun tallafa wa Bouhlel da ya kaddamar da harin na ta’addanci a birnin na Nice.

Molins ya ce mutane biyar cikinsu maza hudu da mace guda akwai hannunsu a harin da suka dauki watanni suna kitsa yadda za su kai shi.

Masu bincike sama da 400 ne suka shiga aiki kan shedun binciken harin tun daga ranar 14 ga watan Yuli inda Bouhlel ya kaddamar da harin rashin imani kan jama’a da ya halaka 84 da raunata wasu 400.

Za dai da tuhumi mutanen da suka tallafa wa Bouhlel da laifin hada baki a aiwatar da ayyukan ta’addanci ban da wasu laifuka.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like