Faransa: Bincike bayan hari a coci


Biyo bayan kisan gillar da aka yi wa wani babban limamin Coci mai mukamin Fada a Faransa da ke da shekaru 85 a duniya, an cafke dan uwa ga wadanda suka hallaka shi.

 

 

Babban mai shigar da kara na Faransan ne ya sanar da hakan, inda ya ce mutumin mai kimanin shekaru 30 a duniya na da masaniya kan harin da Abdel Malik Petitjean ya kai. A cewar wani jami’in dan sandan Faransan shaidun da aka samu a cikin na’urarsa ta Computer da ma wayarsa ta salula, sun nunar da cewa ya san abubuwa da dama dangane da shirye-shiryen kai harin. Rahotanni sun nunar da cewa wani ya kawo musu ziyara a watan Yunin da ya gabata, kana sun dunguma zuwa Siriya tare da Petitjean kafin daga bisani ya dawo. A ranar Talatar makon da ya gabata ne dai Petitjean da ke da shekaru 19 a duniya tare da wani da ya taimaka masa suka kai hari a Cocin Saint-Étienne-de-Rouvray tare da yi wa babban limamin majami’ar Jacques Hamel yankan rago bayan da suka yi garkuwa da wasu mata uku da ke cikin cocin kafin ‘yan sanda su kawo dauki.

You may also like