Faransa da Birtaniya sun budewa ‘yan gudun hijira marayu kofofinsu


 

Kasashen Faransa da Birtaniya sun bude kofofinsu ga ‘yan gudun hijira marayu.

Mataimakin ministan harkokin cikin gida na Birtaniya mai kula da al’amuran gudun hiira Robert Goodwill ya fitar da sanarwa game da wannan batu inda ya ce, sakamakon rufe sansanin Calais a Faransa sun amince da kasar don karbar yara kanana da ba su da iya ye.

Goodwill ya ce, ya zuwa yanzu Birtaniya ta karbi yara kanana sama da 750 daga Faransa.

Ya ce, sun aike da mafi yawan yaran zuwa ga makusantansu da ke Birtaniya. Wadanda ba su da kowa kuma an mika su ga gidajen raino.wadanda suka rage a Faransa kuma gwamnatin kasar na kula da su.

Goodwill ya kara da cewa, daga yanzu za su ci gaba da karbar yara kanana da ba su da kowa daga hannun Faransa.

You may also like