Shugaban Faransa Francois Hollande ya tabbatar da mutuwar sojojin kasar guda uku wadanda ke aikin tattara bayan sirri a kasar Libya.
Hollande ya ce, sojojin sun gamu da hadari ne lokacin da suke aikin tattara bayanan sirri mai sarkakiya a kasar Libya sakamakon faduwar jirginsu.
Kasar Faransa na daga cikin kasashen da suka jagoranci kungiyar NATO wajen taimaka wa ‘yan tawayen Libya kifar da gwamnatin shugaba Muammar Ghadafi a shekarar 2011.