
Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Faransa za ta buga wasan karshe a Gasar Kofin Duniya a Qatar ranar Lahadi da Argentina, bayan da ta taka wa Morocco burki a wasan daf da karshe.
Ranar Laraba Faransa mai rike da kofin da ta dauka a Rasha a 2018 na biyu jumulla ta ci Morocco 2-0 a filin wasa na Al Bayt.
Minti biyar da fara wasa Faransa ta ci kwallo ta hannun Theo Hernandez kuma haka suka je hutu.
Saura minti 11 a tashi daga karawar Randal Kolo Muani ya ci wa mai rike da Kofin Duniya na biyu a wasan.
Karon farko da Faransa ta yi wasa ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, bayan wasa 11 da ta yi tun daga watan Yuni.
Wannan kuma shi ne karon farko da kwallo ya shiga ragar Morocco a Qatar, bayan da ta ci gida a wasa da ta doke Canada 2-1 a cikin rukuni.
Faransa ta kawo wannan matakin bayan da ta ja ragamar rukuni na hudu da maki shida, wanda ya hada da Australia da Denmark da kuma Tunisia.
A zagaye na biyu Faransa ta ci Poland 3-1, sannan ta doke Ingila 2-1 a karawar daf da na kusa da na karshe.
Morocco ita ta ja ragamar rukuni na shida da maki bakwai da ya hada da Croatia da Belgium da kuma Canada.
Asalin hoton, Getty Images
Morocco ta yi nasara a kan Sifaniya a bugun fenariti 3-0, bayn da suka tashi ba ci, sannan ta yi nasara a kan Portugal da ci 1-0 a Quarter finals.
Wannan shi ne wasa na biyar da suka fafata a tsakaninsu, kuma na farko a Kofin Duniya, inda Faransa ta ci biyu da canjaras biyu.
Wasa na karshe da suka hadu tsakanin Faransa da Morocco shi ne ranar 16 ga watan Nuwambar 2007, inda suka tashi 2-2 a wasan sada zumunta.
Haka kuma Faransa ta zama ta farko da ta kai wasan karshe a Gasar Kofin Duniya karo biyu a jere tun bayan Brazil a 2002, kuma ta farko a Turai tun bayan bajintar Jamus a 1990.
Wasan karshe na hudu da Faransa za ta yi a Gasar Kofin Duniya bakwai baya, kenan a1998 da 2006 da 2018 da kuma 2022.
Tawagar Faransa na fatan zama ta farko da za ta kare kofinta na Duniya tun bayan shekara 60, bayan bajintar da Brazil a 1958 da kuma a 1960, sai dai Italiya ce ta fara hakan a 1934 da kuma 1938.
Didier Deschamps shi ne na hudu da ya ja tawaga kai wa zagayen karshe karo biyu a jere.
Kociyoyin da suka yi wannan bajintar sun hada da Vittorio Pozzo tare da Italy a 1934 da kuma 1938, sai Carlos Bilardo tare da Argentina a 1986 da 1990 da kuma Franz Beckenbauer da tawagar Jamus a 1986 da kuma 1990.
Ranar Lahadi Argentina za ta kara da Faransa a wasan karshe, kafin nan Croatia da Morocco za su fafata a wasan neman mataki na uku ranar Asabar.