Faransa : ‘Yan Bindiga Sun Jikkata Mutum 8 Gaban Wani Masallaci


Wasu ‘yan bindiga sun jikkata mutum takwas a gaban wani masallaci dake birnin Avignon a kudu maso gabashin kasar Faransa.

Rahotanni daga kasar sun ce mutane biyu ne a cikin wata mota suka bude wuta kan mutanen dake gaban masallacin inda suka jikkata takwas daga cikinsu ciki har da wata karamar yarinya.

Bayanai sun ce babu abun damuwa akan halin da mutanen da suke ciki.

Sai dai hukumomnin shari’a a yankin sun ce lamarin bai da wata alaka da ta’addanci, kuma tuni aka mika binciken ga ‘yan sanda.

Harin dai na jiya na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wani ba’amurke dan sheklaru 43 ya nemi aukawa wasu masallata da mota a gaban wani masallaci dake lardin Creteil a kudu maso gabashin birnin Paris.

Tun dai harin kyammar musulmi na birnin Landan da ya yi sanadin jikkatar mutane 11 a ranar 19 ga watan Jiya al’ummar musulmi a Faransa ke jin suma suna fuskantar barazana, inda suka bukaci hukumomin kasar dasu karfafa masu matsakan tsaro a wuraren ibada.

You may also like