Yayinda manoma ke girbe alkama a Jahar Kano bincike yanuna cewa farashin Alkama ya karye a Jahar Kano.
A babbar kasuwar abinci ta duniya dake, Dawanau a kwanakin baya ana sayar da buhunta akan kudi Naira dubu talatin da hudu (34000) amma a yanzu farashin yakoma Naira dubu goma sha biyar(15000).
Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Dan Liti yace wannan shine faduwar farashi mafi kankanta da aka samu a tarihi.
Malam Mahe waziri wani manomin rani yace hakika wannan shi ake kira ambaliyar kasuwa.