Farashin Burodi Ya Karu Da Kaso 15 Cikin DariHadin gwiwar kungiyar masu sarrafa burodi da abinci dangin fulawa sun bayyana karin farashin burodi da kaso 15 cikin dari.

Karin farashin wanda ya bullo a shiyyar Arewa Maso gabashin kasar nan ya biyo bayan hauhawar da ake samu na farashin kayan sarrafa burodin,kamar yadda kungiyarta bayyana.

‘Yayan kungiyar sun ce ya zama dole su yi wannan kari indai har su na son ci gaba da yin sana’ar.

Kungiyar ta ce ta yi la’akari da halin kuncin da ake ciki a kasar a yayin da take yin karin, inda ta ce Biredin Naira N60 a yanzu ya koma Naira 70, na N120 ya koma N140, sai kuma wanda ake sayarwa N200 ya koma N240.

Kungiyar ta kuma gargadi ‘yayanta game da rage girman burodin da suke sarrafawa akan wannan sabon farashin.

You may also like