Farashin danyen mai ya tashi a Duniya


 

Farashin danyen mai ya tashi zuwa dala 51 yayin da akesa ran kungiyar OPEC za ta taƙaita yawan man da take haƙowa.
Kudin gangan ɗanyen mai ya ƙaru ne a kasuwar hada-hada ta London, a wani bangare na matakin da masu zuba jari suka fara ɗauka a ranar Juma’a.

Hakan na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa, Saudiyya da Iran zasu ɗinke ɓarakar da ke tsakaninsu, domin tunkarar cushewar da aka samu a kasuwar man ta duniya.

A watan gobe ne ake sa ran ƙungiyar kasashe masu arzikin man fetur na duniya, OPEC za ta yi taron gaggawa a Algeria.

Su ma ‘yan kasuwa sun ƙara farashin man ne, bayan da wasu bayanai da aka tattara a Amurka ke nuna cewa, man da take adanawa don gobe ya ragu, saboda buƙatar man ta ƙaru.

Hakazalika akwai yuwuwar Rasha wadda ba ta cikin ƙungiyar OPEC ta bayar da haɗin kai wajen taƙaita yawan man da take haƙowa.

You may also like