Farashin Danyen Man fetur ya tashi a kasuwar Duniya. 


NNPC NIGERIA 🇳🇬

Farashin danyen man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan kasashen da ke da arzikin man fetur na kungiyar OPEC sun amince su rage yawan man da suke hakowa.
Wannan ne dai karo na farko da kasashen suka dauki irin wannan mataki a cikin shekaru 8, wanda aka dauka da nufin magance matsalar faduwar farashin da ake fuskanta.
Sun cimma hakan ne a taron da suka yi ranar Laraba a birnin Algiers na Algeria.
Fahimtar junanan da aka cimma za ta share fage kan yarjejeniyar da da ake fatan kungiyar zata cimma a taron da za ta yi a watan Nuwamba mai zuwa.

Farashin man ya tashi da kashi shida cikin dari, sakamakon wannan mataki na kungiyar ta OPEC.

Haka kuma hannayen jari a kasuwannin duniya sun fara tashi su ma, sakamakon amincewar rage yawan man da ake hakowa.
Ana fatan matakin zai sa kasahen da suke fama da matsalar tattalin arziki za su farfado.

Kasashe irin su Najeriya da Venezuela da Saudiya na daga wadanada faduwar farashin mai ta janyowa karayar tattalin arziki, kuma ake fatana matakin zai taimake su.

You may also like