Farashin gangar danyen mai ya fadi ƙasa da $3 cikin mako guda a kasuwar duniya


Farashin gangar ɗanyen mai nau’in Brent ya yi ƙasa da $3.31 tsakanin ranakun Litinin zuwa Juma’a bayan da farashin ya kwashe makonni yana yin sama.

A tsakar ranar Litinin ana sayar da kowacce ganga kan dala $67.68 faduwar $2.32  daga  $70 farashin da aka sayar da shi a ƙarshen watan Janairu.

Ya zuwa tsakar ranar Juma’a farashin ya ƙara yin ƙasa zuwa dala $64.37 bayan da aka fara samar da mai daga ƙasar Amurika inda hakan ke neman kawo barazanar yawan man fiye da yadda ake buƙata a   kasuwar mai ta duniya.

A shekarar 2016 ne ƙasashe mambobin ƙungiyar ƙasashen masu albarkatun mai OPEC dama waɗanda bana ƙungiyar ba suka cimma yarjejeniyar rage man da suke fitarwa a kowace rana a ƙoƙarin da suke na sai-saita farashinsa.

Duk da cewa kasafin kudin Najeriya baya fuskantar barazana daga faduwar man a kasuwar duniya saboda anyi kiyasin kasafin kudin kan farashin $45 ko wacce ganga amma hakan zai shafi kuɗin da ake tarawa a asusun ajiye rarar mai.

You may also like