Farashin garin rogo yayi kasa da kaso 60


Farashin garin kwaki wanda na daya daga cikin abincin da ake yawan amfani dashi a kasarnan ya fadi kasa da kaso 60, a Enugu cikin watanni huɗu.

Wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa wanda ya zagaya ta kasuwanni ya lura cewa farashin ya fadi  daga ₦1200 kan yadda ake siyar da bokitin fenti a baya zuwa ₦450 zuwa ₦500.

Ƙaramin bokitin fenti shine mudun da ake amfani da shi wajen awo a yankin kudu maso gabas.

Ya wancin masu siyayya da suka zo kasuwar sun bayyana farin cikinsu saboda yanzu suna iya siyan farin gari akan ₦450 yayin da farashin jan gari yake ₦500.

Wasu yan  kasuwa sun alakanta faduwar farashin da yadda aka samu albarkar kakar  rogo a bana.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like