Alkaluman tattalin arziki sun nuna cewa farashin kayayyaki a Najeriya ya yi tashin da bai taba yi a kusan shekara goma da suka wuce.
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar sun bayyana cewa farashin kayayyakin ya karu da kimanin kashi 16.5 a watan Yunin da ya gabata.
Hakan dai ya nuna girman rikicin tattalin arzikin da kasar ta ke ciki.
Hukumar ta kara da cewa farashin lantarki da sufuri da kayan abinci ya yi matukar tashi saboda darajar kudin kasar, Naira, ta ci gaba da faduwa idan aka kwatanta da Dalar Amurka, lamarin da ya sa kayan da ake shiga da su kasar ke ci gaba da yin tsada.
Tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne kacokan a kan man fetur, sai dai farashinsa ya yi matukar faduwa a kasuwannin kasashen duniya, lamarin da ya yi matukar shafar kasashen da ke fitar da man na fetur.
Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya ta yi gargadin cewa tattalin arzikin Najeriya zai gamu da cikas a wannan shekarar – a karon farko cikin shekara 20 – saboda faduwar farashin man fetur da karancin wutar lantarki.