Kamfanin Dillancin Labaru na Nijeriya ya ruwaito cewa farashin kayayyakin abinci sun fara tashi a jihar Katsina a daidai lokacin da aka doshi watan Azumin Ramadan.
Sakamakon wani bincike da kamfanin Dillancin labarun ya gudanar ya nuna cewa kayayyakin abincin da farashin ya fara tashi sun hada da shinkafa, wake, Gero, Masara da kuma garri.
Binciken ya nuna cewa buhun wake mai kilogram wanda ake sayarwa a kan Naira 20,000 a halin yanzu ya kai kusan Naira 40,000 sai buhun Gero wanda a watanni uku da suka wuce ake sayarwa N 8,000 a halin yanzu farashinsa ya kusa kai N 16,000.
Sai dai kuma Shugaban Dillalan Sayar da Hatsi na jihar, Alhaji Ahmed Musa ya bayyana cewa an samu tashin farashin kayayyakin abinci ne sakamakon karancin man dizil wanda manyan Motocin da ke jigilar kayayyakin ke amfani da shi.