Farashin Kayan Abinci Ya Karye A Kano


 

Farashin kayan abinci a halin yanzu ya sakko a wasu daga kasuwannin jihar Kano tun bayan da aka yi girbi kuma sabon kayan abincin na bana ya shigo kasuwa, kamar yadda wani bunciken gani da ido ya tabbatar.

A ziyarar da wakilinmu na Kano, Abubakar Haruna Galadanchi, ya kai ziyara wadansu kasuwannin sayar da hatsi na jihar Kano da suka hadar da kasuwar Dawanau, kasuwar Sharada ‘yan rake, kasuwar Sabon Gari da kasuwar Kurmi, ya ganewa idanunsa cewar, da yawa daga kayan abinci dangi hatsi, da suka hadar da masara, gero, shinkafa ‘yar Hausa da dai sauransu, farashinsu ya sakko da kusan kaso 40 bisa 100 na farashin da ake sayar da su a watannin baya.

Zagayan gani da idon kasuwannin har wayau ya gano cewar, buhun masara a halin yanzu ana sayar da shi akan Naira 8,500 a madadin 12,500 a watan daya gabata, hakazalika buhun gero, shi kuwa da a baya ake sayar da shi akan kudi Naira 14,000, yanzu haka ya dawo Naira 9,500.

Ita kuwa shinkafa, da ake nomawa a nan gida a baya kudinta ya yi tashin gwauran zabi har na kusan Naira 40,000 amma a halin yanzu kuwa ta sakko zuwa Naira 28,000 zuwa 26,000. Inda ake aunar da kwano guda akan Naira 600 a madadin Naia 750 da ya ke a watan jiya.

Ita kuwa  alkalam wadda farashinta ya kai Naira 24,000, a halin yanzu ta sakko zuwa Naira 16,000.

Hakazalika, wasu al`ummar jihar Kano sun bayyana farin cikinsu dangane da hakan inda suka ce babu shakka wannan sauki da aka samu ba karamin dadi talaka zai ji ba musamman la`akari da yadda rayuwa ta yi tsada matuka da gaske, inda suka yi kira ga gwamnatin tarayyya da ta sake waiwayar manoma yadda ya kamata da kayan noma na zamani, wanda hakan zai taimaka a samu abinci yadda ya kamata kuma kasa ta zauna lafiya.

Shi kuwa wani dan kasuwa a kasuwar hatsi ta Dawanau, Alhaji Ismail Alhassan Isyaka, cewa ya yi lallai manoma suna kokari kuma saukar farashin kayan abincin ba zai rasa nasaba da shigowar sabon kayan abincin da su manoman suka noma ba, wanda ya ke shigowa kasuwa a kullum daga gonaki.

Hakan ya sanya kayan abinci ya yawaita a kasuwanni wanda yawaitarsa ya haifar da karyewar farashinsa.

You may also like