Farashin Kayayyaki Na Tashin Gwauron Zabi A Kasuwar Duniya –  NBS 



Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta yi ikirarin cewa a halin yanzu farashin kayayyaki a kasuwanni ya yi matukar tashi da kashi 18.48 cikin 100 wanda ba a taba samun haka ba a tsakanin shekaru 11 da suka wuce.
A cikin wani bayani da hukumar ta fitar ta nuna cewa farashin kayayyakin abinci na ci gaba da tashi a kasuwanni inda ta nuna cewa kayayyakin da farashinsu ya fi tashi sun hada da, burodi, kifi, Nama, man yin girki, da kuma Hatsi.

You may also like