Farashin Masara Ya Soma Karyewa A KasuwanniKamar yadda muke ji labarin ana saida masara cikin sauki a garuruwan Kazaure a Jigawa, Danbatta dake Jihar Kano da sauran wasu yankuna, yau abun ya zo garin Daura. Inda ake siyar da tiya akan farashin naira 270, buhu kuma a farashin naira 10,700. 

Ana sayarwa a Kangiwa Kofar Fada da kuma shatale-tale na Tashar Kudu da tashar yamma da kuma kasuwa.

Allah kara kawo mana sauki. Allah kaba ‘yan kasuwarmu ikon tausaya al’umma, ka kara haskaka kasuwancisu, mu kuma Allah ka ba mu ikon saye da karfin arziki.

You may also like