Farashin lemuka nau’in giya da kuma taba sigari zai karu bayan amincewa da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi na gyara da aka yi wa dokar haraji.
Tun a kwanakin baya ne ministar kudi Kemi Adeosun ta rubutawa shugaban kasar wasika inda ta nemi amincewarsa domin a sake d’aga harajin.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a ranar Lahadi, sabon harajin zai fara aiki daga ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2018.
A sanarwar Adeosun ta bayyana cewa sabon kudin harajin za a raba shi zuwa shekaru uku domin sai-saita illar da hakan zai kawo kan farashin kayayyakin.
Ministan ta ce sabon karin harajin zai kara samarwa da gwamnati kudaden shiga kuma zai sa a rage ta’ammali da kayayyakin saboda illar da suke da shi ga lafiya.
Karakashin sabon harajin kowanne karan sigari za a kara masa ₦ 1, a shekarar 2018 kenan a kowane kwali za a kara ₦20. A shekarar 2019 zai karu zuwa ₦40 a kowanne kwali ya yin da a shekarar 2020 za zama ₦58.